ATM wanda ake kiraAutomated Teller Machine na’ura ce da ake amfani da ita domin diban kudi ko aikawa da sakon kudi ga mutumin da yake ma’ajiya a daya daga cikin bankunan da suke amfani da wannan tsari ba tare da neman taimakon wani ma’aikacin banki ba. Irin wannan na’ura da ake kira da ATM iri biyu ce. Akwai wacce ita aikin ta shine ta bayar da kudi kawai sannan kuma zata iya bayar da bayanan kudi ko rahoton abin da mutum ya ajiye a bankinsa.

Dayar kuwa tana aikin da ya zarce ta farko domin baya da biyan kudi kuma tana ba mutum damar ya iya aikawa da sakon kudi na zahiri, da bayar da wadansu muhimman bayanai na katin ATM din mutum sannan kuma ya fitar rahoton bayanan bankin mutum.

Shi wannan na’ura na ATM bankuna ne kawai suke amfani da su domin biya da fitar da bayanan mutane. Su kuma abokanan huldarsu suna iya amfani da wannan na’ura ce kawai idan suka karbi katin ciran kudi daga bankin nasu.

Shi kuma wannan katin ajikinshi akwai wata ‘yar karamar na’ura da ajikinta akwai maganadisu da yake tattare da bayanai na babban kwamfutocin shi wannan banki da ake amfani da shi wurin sanin me mutum ke ajiye da shi a mazubinshi.

Da wannan dalilin ne ya sa mutum ke saka wannan katin a jikin wannan mashin na ATM ya iya fitar da kudin dake cikin akwatinsa bayan ya saka lambobin sirri guda hudu da bankinsa suka bashi idan komai yayi daidai kudi ya fito daga na’urar iya adadin abinda yake bukata.

Wannan na’ura ta ATM John Shepherd-Barron ne ya kirkire ta a shekarar 1960

ABUBUWAN DA SUKA HADA ATM


Na’urar ATM ta hada abubuwa manya guda biyu

1.Abubuwan shigar da bayanai (Input Devices) 1.Na’urar karanta bayanan kati – Card Reader 1.Na’urar Rubutu – Keypad 2.Abubuwan fitar da bayanai (Output Devices) 1.Na’urar fitar da sauti – Speaker 1.Na’urar nuna rubutu – Display Screen 1.Na’urar fitar da takarda – Receipt Printa 1.Na’urar fitar da kudi – Cash Dispenser Na’urar Karanta bayanan kati – Card Reader