A dai wannan shekara har wa yau kuma sai ga wata fasahar sabuwa ful, mai suna: “Super Density” Disc, wato “SD” kenan a taqaice. Waxanda suka samar da wannan fasaha dai kamfanoni ne guda 7, kuma su ne kamar haka: Toshiba, da Time Warner, da Matsushita Electric, da Hitachi, da Mitsubishi Electric, da Pioneer, da Thomson da kuma JVC.

Waxannan dai kamfanoni ne na qere-qere a fannin lantarki da sadarwa. Kuma ta la’akari da wancan sabuwar fasaha ta MMCD, akwai savabin tsari da yanayin taskance bayanai. Wannan na nufin idan an fara qera faifan wannan fasaha za a samu matsala kenan. Ana cikin haka sai haxakar kamfanonin kwamfuta guda biyar, a cikin watan Agusta na shekarar 1995, suka yi zuga don nuna rashin amincewarsu da wannan tsari bambarakwai, wai namiji da sunan Rakiya. Waxannan kamfanoni dai su ne: kamfanin IBM, da kamfanin Apple, da kamfanin Compaq, da kamfanin Hewlette-Packard, sai kuma kamfanin kwamfuta na Microsoft.

Waxannan kamfanoni dai sun qi amincewa ne da savanin dake tsakanin waxancan fasahohi guda biyu, kuma suka ce dole ne a hade tsarin wadannan fasahohi guda biyu don samun tsari bai-xaya. Wannan gungu na kamfanonin kwamfuta dai sun naxa shugaban kamfanin IBM ne don jagorantar wannan kwamiti don tabbatar da samuwar biyan buqatarsu. Kuma cikin dacewar Allah, nan take aka samu amincewar kowane vangare; aka tabbatar da kundin fasahar DVD mai xauke da tsari xaya, da taskancewa da kuma sarrafa bayanai ta hanyar dukkan na’urorin da za a qera don aiwatar da hakan.