Smartphone ko kuma kace wayoyin-komai-da-ruwanki kamar yadda malamina Mal. Abdullahi Salihu Abubakar Baban Sadik ke fassarawa wayoyi ne kirar selula (cellular telephone) wacce aka hada ta da kwamfuta a wurin yin aki da wadansu karin aikace aikace da aka san wayoyin hannu a dabi’ance basa yi. Misali kamar saka mata babbar manhaja (Operating System), da manhajar shiga internet (browser) da kuma karfinta wurin amfani da manyan manhajojin da kwamfuta aka sani a dabi’a suke yi.

Smartphone ta farko ita ce IBM’s Simon, wacce suka gabatar da ita ba a matsayin wayar yan kasuwa ba a wani buki na baje kolin kayan kwamfuta a shekarar 1992 mai suna COMDEX Computer Trade Show.

Ita wannan wayar ta IBM’s Simon a lokacin tana iya aikawa da imel da faks, tana kuma iya ajiyar kwanan wata da bayanan alkawuran mutum bayan iya kira da aikawa da sakon kar ta kwana. Karawa kayan lantarki na taimakon dan adam a aikace-aikacensa na yau da kullum (Personal Digital Assitants – PDA) a karni na 21 lokacin da irin wadannan kayan lantarki na PalmPilot aka kara mata fasahar Wireless domin samun shiga intanet shi ya canza komai.
A shekarar 1996 kamfanin Nokia da HP suka sanyawa PDA dinsu damar kiran waya da kuma saka musu babar manhaja ta farko (OSes) da kuma damar shiga Intanet ta hanyar amfani da Browser.
A tsakiyar shekarar 2000 kamfani Blackberry ya fito da cikakkiyar wayar farko da aka kira ta da Smartphone a kasuwa dalilin haka yasa wayar ta shahara a Duniya baki daya. A shekarar 2007 kamfanin LG ya fito da tashi wayar mai suna Prada sannan duk a wannan shekarar kamfanin Apple ya fito da tashi mai suna iPhone, wacce ita ce Smartphone ta farko dake da tsarin taba fuska ba maballi.

Bayan shekara guda kamfanin HTC ya fitar da shima tashi smartphone din wacce ta fara zuwa da Babbar Manhajar Android na Google.

Daga cikin manyan cigaban da aka samu wurin kirkirar wayoyin komai-da-ruwanki wanda tarihi ba zai manta ba ya hada da wacce kamfanin Sony ya fitar mai suna Xperia Z5 Premuim wacce take zuwa da tsarin daukar hoto mafi girma a waya a wancan lokacin da take daukar hoto 4K a shekarar 2015.

Samuwar Wi-Fi da LTE shima cigaba ne a duniyar smartphone a cikin wadannan shekarun wanda ya taimaka wurin samun saurin musayar bayanai ga masu amfani da su.