A ranar Litinin ne daya daga cikin ma su jinyar korona da aka sallama daga cibiyar killacewa a jihar Delta ta yi zargin cewa damfara kawai ake yi da sunan cutar a Najeriya.
Matar, mai shekaru 36, ta kamu da cutar korona a ranar 17 ga watan Afrilu bayan an yi jayayya da ita a kan sakamakon gwajin kwayar cutar da aka yi mata.
Daga bisani an dauketa zuwa cibiyar killace ma su cutar korona da ke garin Warri, inda ta shafe kwanaki 17 ta na jinya kafin daga karshe a sallameta.
Yayin ganawarta da manema labarai bayan an sallameta, matar ta kafe a kan cewa damfara kawai ake yi da sunan cutar a Najeriya, saboda har yanzu ba ta ga sakamakonta da ya nuna cewa ta na dauke da kwayar cutar ba.
"Ta sakon radiyo aka sanar da ni cewa na kamu da cutar. Kira na aka yi aka sanar da ni ba tare da bani wani rubutaccen sakamako ba. Tun kafin su tafi da ni cibiyar killacewa na sanar da su cewa babu kwayar cutar a kasar nan," kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito matar na fada.
"Ba za a iya shawo kan cutar ba idan da gaske akwai ta a kasar nan. Watakila akwai ta a nahiyar Turai, amma babu ita a nan. An ajiyeni a cibiyar killacewa ba tare da amincewa ta ba.
"Har yanzu ana cigaba da samun cunkuso a kasuwanni da bankuna, idan da gaskene cutar ta shigo kasar nanda mutane da yawa sun kamu. Damfara ake yi da sunan cutar a Najeriya.
"Ni shaida ce, na je kuma na gani. Ban yarda na kamu da cutar korona ba duk da an kai ni cibiyar killacewa a matsayin mai jinya.
"Abokina da mu ke zaune tare kafin a kai ni cibiyar killacewa ya cigaba da rayuwarsa a gida. Sakamakon gwaji bai nuna ya kamu da cutar ba. Ina batun sauran dangina da mu ke tare a gida?
"Mahaifiyata ce ke min wanka, sannan ta kwana tare da ni lokacin da bani da lafiya. Shekarar mahaifiyata 70 a duniya, amma duk da irin kusancinmu ba ta kamu da cutar ba, ta cigaba da rayuwarta a gida.
"Ba su shirya wasan kwaikwayon ba sosai su amma su ka fara nuna shi. Kamata ya yi su binciki dukkan iyalina. Hatta Sakamakon da ake yadawa a kan cewa likitocin da ke duba lafiyata sun kamu da cutar duk karyane, shirya abin su ka yi,"a cewar matar.
Terima kasih sudah membaca artikel: "Korona a Najeriya damfara ce kawai - Ma su jinyar da aka sallama"
Entry artikel sejenis mungkin tersedia di blog ini, periksa: Related Posts.
Entry artikel sejenis mungkin tersedia di blog ini, periksa: Related Posts.
Comment
All comments under post "Korona a Najeriya damfara ce kawai - Ma su jinyar da aka sallama"
Related Posts: